Labarin dake shigo mana daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar mutane da dama ne suka mutu, wasu kuma suka samu raunuka bayan da wata babbar motar dakon kaya ta kufce ta fa?a kan mutane a garin Jimeta.
Wani da lamarin ya faru a gabansa ya shaida wa BBC cewa mutum 11 ne suka mutu nan take sakamakon hatsarin.
Sai dai shugaban Hukumar kare afkuwar ha?urra ta Najeriya reshen jihar Adamawa ya ce gaba ?aya mutane 15 ne lamarin ya rutsa da su.
Ya ?ara da cewa sun gano cewa lalacewar burki ne ya haifar da ha?arin.
Motar ta ?wace ne ta haye kan wasu motoci kafin ta fa?a wani garejin kanikawa a maha?ar Vunoklang.
Rundunar ?an sanda a jihar ta Yola ta ce an kai mutanen da suka samu raunuka asibiti.
