An Shiga Ya?in Cacar Baki Tsakanin Kwankwaso Da Tambuwal

Sabon rikici na ya?in cacar baki ya kunno kai a babbar jam’iyyar adawa ta PDP reshen arewa maso yamma, tsakanin tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya Rabi’u Kwankwaso da Gwamnan Sokoto Tambuwal.

Rahotanni sun bayyana cewar Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da yin katsalandan a harkokin jam’iyyar a jihar Kano, ta hanyar shiga sharo ba shanu.

Kwankwaso wanda ya kasance daya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar a yankin ya zargi Tambuwal da hada kai da wasu ya’yan jam’iyyar na Kano da ke adawa da shi da mutanensa don taimaka musu su samu shugabancin jam’iyyar na Arewa maso Yamma.

A hirarsa da sashin Hausa na BBC Kwankwaso ya ce: “Abin takaici shi ne kalaman gwamna na Sokoto, wanda a ra’ayinsa yace bai kamata mu musamman mu ‘yan Kwankwasiyya a bamu wadan nan mukamai ba.”

“Kwarai da gaske abunda ya faru abunda muke da shi mu da Jigawa shine muna da shugaba na wannan sashi. “Toh babban matsalar shine a cikinmu akwai wadanda aka samu matsaloli da su, cewar sun yi mana zagon ?asa a jam’iyya.

“Toh saboda haka da wannan fom ya shigo ni na tura an siyo mana fom, amma abunda ya sa magana ta fito na shi Tambuwal, ya siye wannan fom a wurin wannan taro da muka yi, an kawo rahoto cewa shine ya bayar da kudi aka siyo masa fom kuma aka ba shi Sanata Bello Hayatu.

” Game da abunda ya kawo Tambuwal harkar siyasar Kano, Kwankwaso ya ce: “Abunda ya kai shi (Tambuwal) shine gaggawa, saboda mutane da yawa suna ganin abunda yake yi ya shafi takarar shekarar 2023.

To sai dai a nasa bangaren, gwamna Aminu Tambuwal ya karyata wannan zargi inda ya ce “duk wanda yake da sha’awa ya fito ya yi takara, to ya fito ya yi takara”. Ya kuma nisanta kansa da zargin da Kwankwaso ya yi masa na cewa yana da hannu a siyawa Sanata Bello Hayatu Gwarzo fom.

Related posts

Leave a Comment