Akwai Hannun Sarakuna Da Manyan ‘Yan Siyasa A Matsalar Tsaron Zamfara – Bincike

Wani rahoto da Jaridar Vanguard ta fitar, ya nuna cewa mutane sama da 6, 300 suka mutu a rikicin Zamfara, sannan an yi garkuwa da mutane 3, 672. A dalilin rikicin, an maida mata 6,483 zawarawa, yara 25,050 sun zama marayu.

An sace shanu 215, 241 da sauran dabbobi 160, 000, an kona gidaje 3, 587. Jaridar Vanguard tace har yau ba a dabbaka mafi yawan shawarwarin da kwamitin da ya binciki rikicin na Zamfara ya ba gwamnatin Bello Matawalle ba.

Da an yi aiki a kan rahoton da kwamitin ya ba gwamna, da an gurfanar da wani tsohon gwamnan jihar, sannan a tsige wasu daga cikin sarakunan da ke jihar.

Haka zalika da an gurfanar da wasu jami’an sojoji 10 a sakamakon zarginsu da hannu a kashe-kashen. Binciken da aka gudanar ya nuna daga cikin abubuwan da suka hura wutan rikicin akwai daukar doka a hannu, da raba wa mutane jeji a matsayin filin noma.

Kuskuren da gwamnoni suka yi Jami’an sa-kai da aka rika kirkiro wa sun rika kashe wadanda ake zargi da laifi. Wannan ya hada fada tsakanin Fulani da mazauna wasu kauyuka a Zamfara.

A lokacin da ‘yan fashi suka addabi jihar Zamfara, sai gwamnatin Ahmed Sani Yariman Bakura ta share jeji domin rika noma a inda ‘yan fashin ke fake wa. Wannan matsaya da gwamnan ya dauka ya jawo rigima tsakanin manoman da masu kiwon dabbobi.

Da Mamuda Aliyu Shinkafi ya zama gwamna a 2007, an rika raba wa manyan gwamnati filaye domin su yi noma. Hakan ya kara jawo aka rasa wuraren kiwo.

Binciken kwamitin ya nuna gwamnatin Abdulaziz Yari Abubakar ta gaza magance matsalar, ta jawo ‘yan bindiga daga nesa suka rika shigo wa jihar Zamfara. Wannan ya sa kwamitin ya bada shawarar a kama gwamna Abdul’Aziz Yari Abubakar da wasu hadimansa; Bello Dankande Gamji, da Sani Gwamna Mayanchi.

Kwamitin sun ba gwamna shawarar ya tunbuke rawanin Sarakuna 15 daga cikin Sarakuna 17 da ke jihar Zamfara, saboda zarginsu da ake yi da hada-kai da miyagu.

Related posts

Leave a Comment