Adamawa: An Yi Kira Ga ‘Yan Najeriya Da Rungumar Akidar Zaman Lafiya

An kirayiyan Najeriya da su kaucewa dukkanin abinda zai kawo rarrabuwar kai a tsakanin su domin samun zaman lafiya dama cigaban kasan nan baki daya.

Alhaji Baba Kano Jada ne yayi wannan kira a lokacinbda yake zantawa da Wakilinmu a Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa.

Baba Kano Jada yace ya kamata ‘yan Najeriya su daina nuna banbancin addini ko kabilanci domin samun hadin kai da zaman lafiya a fadin Najeriya.

Baba Kano yace nuna banbanci addini ko kabila ba abinda zai haddasa illa koma bayan zaman lafiya dama cigaban kasan nan baki daya.

Don haka ne ya shawarci ‘yan Najeriya da suyi dukkanin abunda ya dace domin samun hadin kai da zaman lafiyaa tsakanin al’umma baki daya.

Harwayau ya shawarci ‘yan Najeriya da su cigaba dayin addu’o’i domin ganin an kawo karshen matsalar tsaro a fadin kasan da kuma neman taimakon Allah madaukakin sarki domin ganin an kammala zaben shekara 2023 lafiya ba tare da matsalaba.

Related posts

Leave a Comment