Tsaro: Ba Lallai A Yi Zabe A Sassan Arewa Ba – Gwamnoni

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wani sabon batu ya fito daga bakin gwamnonin Najeriya, inda suka bayyana ra’ayin cewa ba lallai a yi zabuka a wasu jihohin Arewa maso Yammacin kasar nan ba saboda kara dagulewar lamarin tsaro a shiyyar.

Arewa maso Yammancin Najeriya dai ta ta kunshi jihohi bakwai da suka hada da; Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto, da Zamfara.

Gwamnonin sun bayyanawa hakan ne a wani taron gaggawa da suka gudanar kan matsalar tsaro dake addabin sassan Jihohin Arewa a Abuja.

A rahoton da suka mika, gwamnonin sun bukaci Buhari ya gaggauta daukar matakai kan alkawurran da ya dauka na magance matsalar rashin tsaro, a yayin ya?in neman za?e da ya yi.

Domin kawo karshen matsalar rashin tsaro, sun shawarci Buhari ya dauki matakin gaggawa, ya kafa sansanin soji a Birnin Gwari, Rijana, Kachia da Mararraban Jos a jihar Kaduna da Kontagora da Gwada a jihar Neja.

Related posts

Leave a Comment