Rahoton dake shigo mana daga Yola babban birnin Jihar Adamawa na bayyana cewar an fara yi wa mata masu fama da cutar yoyon fitsari aikin fida kyauta.
Aikin fi?an na gudanane karkashin kungiyar “Fistula Foundatio” wanda Alhaji Musa Isa ke jagoranta tare da hadin gwiwar ma’aikatan kiwon lafiya ta jihar Adamawa.
Ana gudanar da aikin ne a asibitin kwararru dake birnin Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa.
Yawancin matan dake dauke da cutar yoyon fitsarin dai sun fitone daga karkara dake sassa daban dabŕn a fadin jahar Adamawa .
Za ayi sama da mako daya ana yiwa majinyatan aiki. Don haka nema ake kira ga kungiyoyi da su kasance masu taimakawa domin ganin an yaki cututtuka da dama a fadin Najeriya baki daya.
