Kwaskwarima A Dokar Zabe: Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar Dattawa ta yi fatali da wani ?udirin neman su ?ara yi wa Sabuwar Dokar Za?e Kwaskwarima, kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi ta yi.

A ranar Laraba ce dai mambobin Majalisar Dattawa suka ?i amincewa da wani ?udiri da aka karanta, domin a yi masa karatu na biyu.

?udirin dai na tafiya ne kafa?a-da-kafa?a da bu?atar Shugaba Buhari ta a sake yi wa Dokar Za?e kwaskwarima, domin a cewar Buhari, ya gano wasu gi?in da babu ha?ora a cikin bakin dokar.

A cikin watan Fabrairu ne dai Buhari ya nemi Majalisar Dattawa cewa ta cire wasu ?udiri na ‘Clause 84(12)’, na cikin Dokar.

Kudirin dai shi ne wanda ya haramta wa duk wani mai ri?e da mu?amin gwamnati na siyasa ya yi za?e ko a za?e shi domin tsayawa wata ta takara a wurin gangamin taron siyasa.

Buhari ya ce dokar ?udirin ya take ‘yancin wa?anda aka hana ?in.

Related posts

Leave a Comment