Tabarbarewar Tsaro: Buhari Ba Ya Runtsawa – Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban ?asa, ta yi martani da bayyana kakkausan harshe dangane da zargin da ake yi wa shugaba Buhari na nuna halin ko in kula akan tsaro a yankin Arewa.

Mai ba Buhari shawara kan ya?a labarai Garba Shehu ya bayanin irin ?o?arin da gwamnatin Buhari ke yi wajen ganin an magance matsalar tsaro.

“Ina tabbatar muku sakamakon halin da ?asa ke ciki yanzu musamman yankin Arewa mai girma Shugaban ?asa bai iya runtsawa sosai, kullum yana cikin nazari da biyu bibiyar hanyar da za a lalubo wajen magance matsalar”.

Garba Shehu ya yi bayanin irin ?o?arin da gwamnatin Buhari ke yi wajen ganin an magance matsalar tsaro. Sannan kuma ya bayyana yadda lamarin ba tun yau ya zama mur?a??e ba.

Haka kuma ya tunatar cewa matsalar ‘yan bindiga ta zama ruwan-dare a Afrika ta Yamma, musamman daga Burkina Fasso, Mali, Nijar da wasu ?asashen da daga can guguwar bala’in ta bugo zuwa Arewacin Najeriya.

Shehu ya yarda akwai matsalolin, amma kuma ya nuna yadda ake ?o?arin kawar da su, kamar yadda ya ce an kusa cin ?arfin Boko Haram.

Related posts

Leave a Comment