?an Najeriya sun sako Shugaba Muhammadu Buhari a gaba da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo musamman a Twitter saboda rashin halartar jana’izar Babban Hafsan sojin ?asa da sojoji 10 da hatsarin jirgin sama ya kashe a Kaduna.
A ranar Asabar a Abuja aka binne Babban Hafsan sojin Najariya Janar Attahiru tare da sojoji 10 da suka mutu a hatsarin jirgin sama a ranar Juma’a yayin wata ziyarar aiki daga Abuja zuwa Kaduna.
Sojojin da suka mutu sun ?unshi Janar guda uku da suka ha?a da Birgediya Janar Kuliya babban jami’in le?en asiri na sojin Najeriya da Birgediya Janar M Abdulkadir da kuma Birgediya Janar Olayinka.
Tun a ranar Juma’a da hatsarin jirgin saman ya faru fadar shugaban Najeriya ta fitar da sanarwa da ke cewa “Buhari ya yi matu?ar ka?uwa game da hatsarin jirgin saman da ya yi sanadin mutuwar babban hafsan sojan ?asa Janar Ibrahim Attahiru da kuma wasu jami’an soja.
Buhari, wanda ministan tsaro Janar Bashir Magashi (mai ritaya) ya wakilce shi wurin jana’izar sojojin, ya yaba wa Janar Attahiru kan jajircewarsa a ya?in da yake jagoranta da masu tayar da ?ayar baya tare da bayyana shi a matsayin “Babban hafsan soji kuma jagoran da ake kwaikwayo da shi.
Duk da wasu manyan jami’an gwamnati da gwamnoni sun halarci jana’izar sojojin amma rashin halartar Buhari ne ya fi jan hankalin ?an Najeriya.
Wasu na ganin mutuwar sojoji babban al’amari ne a Najeriya, kuma rashin halartar shugaban ?asa da mataimakinsa ya nuna rayuwar sojojin ba komi ba ne.
Wasu kuma masu mayar da martani na bayar da dalilai na tsaro da annobar korona a matsayin abin da ya sa shugabannin suka ?auracewa wurin jana’izar sojojin yayin da kuma wasu suka ce ba sa?a doka ba ne don shugaba bai halarci jana’iza ba.
Wasu kuma na ganin mahawarar da ake ba ta da wani amfani, abin da ya fi amfani ga ?an Najeriya shi ne jimami da kuma yi wa ?asa addu’a kan wannan babban rashin sojojin da aka yi.
