Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hedkwatar tsaro ta kasa ta bayyana dalilin da ya kawo tarwatsewar jirgin sama wanda yayi sanadiyyar mutuwar shugaban sojojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da wasu sojoji 10 a ranar Juma’a, 21 ga watan Mayun 2021.
Kamar yadda Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun hedkwatar tsaro ya sanar, duk da ana cigaba da binciken sanadin lamarin, hatsarin ya auku ne bayan jirgin ya sauka a filin sauka da tashin jiragen saman na Kaduna.
Nwacukwu ta shafin hedkwatar tsaron na Twitter, ya bayyana cewa Janar Lucky Irabor, shugaban ma’aikatan tsaro ya bada umarnin binciken lamarin da ya kawo mummunan hatsarin.
Mai magana da yawun hedkwatar tsaron yace: “Mummunan lamarin ya faru ne bayan saukar jirgin a filin sauka da tashin jiragen sama na Kaduna saboda yanayin gari mara kyau.
“Shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor ya bukaci bincike domin gano dalilin da ya kawo hatsarin. “A yayin da muke fatan rahama ga zakakuran dakarun sojin da shugaban sojin kasan, AFN na bukatar goyon bayanku da kuma fahimta daga dukkan ‘yan Najeriya a kan wannan lamarin da ya faru.”
