An bayyana cewar duk da halin bore da kiraye kirayen da wasu sassa na kasar nan ke yi akan raba Najeriya, kasar ba zata wargaje ba kamar yadda suke bu?ata Najeriya za ta cigaba da zama a matsayin dunkulalliyar ?asa.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna mai suna Injiniya Khailani Muhammad a yayin tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Liberty dake birnin tarayya Abuja a shirin “State Of The Union” wanda ke zuwa kai tsaye a kowace ranar Lahadi.
Khailani ya kara da cewar babu shakka an samu tada kayar baya daga ?angarorin dake kiran raba Najeriya tun daga kan yankin Inyamurai dake han?oron kafa kasar Biyafira har zuwa kan Yarbawa masu fatan kafa kasar Oduduwa, amma gaba dayansu babu wanda hakarshi za ta cimma ruwa, domin Najeriya za ta cigaba da zama a matsayin dunkulalliyar ?asa da yardar Allah.
Injiniya Khailani Muhammad wanda ya yi takarar Kujerar Gwamnan jihar Kaduna a shekarar 2007 ya ?ara da cewar Najeriya ba zata lamunci sake tsunduma cikin wani ya?i na basasa ba tare da cewar a yanzu haka tana fuskantar wani ya?i na cikin gida, inda ya ja kunnen masu wancan kira da su shiga hankalinsu.
Dangane da batun sake fasalin ?asa kuwa Injiniya Khailani ya ce ko ka?an bai yadda da wannan mataki ba kuma ba zai amfanar ba saboda manyan dalilai, inda ya bayyana cewar da akwai ?ananan ?abilu dake yankunan Inyamurai da Yarbawa wa?anda suke korafin an danne su, kuma mafita ?aya a garesu ita ce Najeriya a matsayin ?asa ?aya, wadannan da sauran wasu matsalolin hujjoji dake nuna batun fasalta ?asa ba zai samu kar?uwa ba a wajen ‘yan Najeriya.
