Sanannen Malamin Darikar Tijjaniya a Tarayyar Najeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya nuna tsananin fushinsa da Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai bisa ga mummunan samamen da jami’an Gwamnatin Jihar suka yi a gidansa a watanni baya inda suka yi awon gaba da daruruwan Almajirai.
Shehin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin sabon Halifan Tijjaniya a tarayyar Najeriya Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II a gidansa dake Bauchi.
?ahiru Bauchi ya bayyana samamen da El Rufa’i ya sa aka yi wa Makaranta Kur’ani da cewa fito-na-fito ne da Alkur’ani da kuma cin fuska a gareshi, saboda bai aikata wani abin da ya cancanci a yi masa hakan ba.
“Ina El-Rufai yake? Na zaci zai kasance daga cikin ’yan rakiyarka, da na umarci masu gadi kar su bari ya yi ko da taku daya habar wannan gidan, saboda shi ne ya tura da jami’an tsaro suka far wa daliban Alkur’ani da karfe 2 na dare a gidana,” inji Sheikh Dahiru Bauchi.
Idan ba a manta ba, jami’an Gwamnatin Kaduna sun taba kai samame a gidan malamin da ke unguwar Tudun Wada, Kaduna, inda suka yi awon gaba da almajiran da ke gidan, bisa zargin cewa tara su a wurin ya saba dokar kariyar COVID-19.
Ya ce, “Sun shigo gidana suna harba hayaki mai sanya hawaye suna tursasa wa wadanda ke ciki saboda kawai masu karatun Alkur’ani ne.
“Sun yi ta bin almajiran a guje, aka kai su wani wuri nesa da gari aka yi watsi da su.
“Har yanzu yawancin wadanda abin ya rutsa da su ba a san inda suke ba,” inji malamin.
Khalifa Sanusi ya nema wa El-Rufai gafara
A kan haka ne Khalifa Sanusi II ya roki Sheikh Dahiru Bauchi ya yafe wa El-Rufai kan abin da ya faru tare da fatan ba za a maimaita irin hakan ba.
