Babban malamin ?arikar Tijjaniya a Tarayyar Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya amince da tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, a matsayin Khalifa.
Shehin malamin ya amince da na?in Sunusi lokacin da tsohon sarkin na Kano ya gabatar masa da takaddar tabbatar da na?insa a hukumance a matsayin Khalifan darikar Tijjaniyya a Najeriya a ziyarar da ya kai jihar Bauchi, kamar yadda ?aya daga cikin ?a?ansa ya tabbatar wa BBC.
A makon da ya gabata aka kawo ?arshen sa?ani da ke tattare da na?in tsohon Sarkin na Kano, Muhammadu Sanusi II, a matsayin jagoran Darikar Tijjaniyya a Najeriya a hedkwatar ?arikar ta duniya dake ?asar Senegal.
Babban jagoran darikar, Mahi Nyass ne ya tabbatar da na?insa lokacin da ya karbi bakuncin tsohon sarkin a wata ziyarar watan azumin Ramadan da ya kai ?asar.
An ambato Sheikh Dahiru Bauchi na cewa na?in na Sanusi bai rusa jagorancin sauran shugabannin darikar Tijjaniyya ba, musamman wa?anda marigayi Shiekh Ibrahim Nyas ya na?a.
Shehin malamin ya yi wa tsohon sarkin na Kano addu’ar jagoranci da kariya ga matsayin da aka ba shi.
Sai yanzu aka na?a sabon Khalifan Tijjaniya a Najeriya tun mutuwar marigayi Sheikh Isiyaka Rabiu a 2018.
Yanzu kuma Sanusi na II ya gaji kakansa Khalifan Tijjaniya na farko a Najeriya, wato Sarki Muhammadu Sanusi I
A watan Maris din 2021 a wani babban taron ?ari?ar da aka gudanar a jihar Sakkwato aka fara tabbatar da na?in tsohon sarkin na Kano a matsayin jagoran ?ari?ar Tijjaniya a Najeriya.
Sai dai na?insa ya zo da ce-ce-ku-ce a Najeriyar inda wasu ?angarorin Tijjaniyar suka ce ba su amince da na?in nasa ba.
Amma yanzu amincewar da Shiekh Dahiru Bauchi ya yi da mabiyansa ya ?ara tabbatar da na?in na Sanusi a matsayin Khalifan Tijjaniya a Najeriya
Rahoton BBC Hausa
