Majalisar dattawan Najeriya ta amince da ?udurin dokar hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ?wayoyi a fa?in ?asar, bayan ?udurin ya tsallake karatu na uku a zauren majalisar.
Majalisar ta amince ta ?udurin bayan kwamitin majalisar kan ayyukan ya?i da fataucin miyagun ?wayyoyi, ?ar?ashin jagorancin Sanata Tahir Munguno ya gabatar da rahotonsa kan sabuwar dokar a zauren majalisar.
Yayin da take sake nazarin dokar, majalisar ta amince da dokar hukuncin kisan ne domin ?arfafa ayyukan hukumar ya?i da fataucin miyagun ?wayoyi ta ?asar.
A lokacin muhuwar, babban mai tsawatarwa na majalisar, Sanata Peter Nwebonyi ya nemi majalisar ta amince da dokar hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ?wayoyin, maimakon ?aurin rai -da-rai.
A lokacin da aka nemi ra’ayin sauran ‘yan majalisar dangane da batun, majalisar ta nuna amincewarta kan dokar ciki har da mataimakin shugaban majalisar dattawan ?asar.
To sai dai wasu tsirarun ‘yan majalisar ba su goyi bayan ?udurin ba, inda Sanata Adams Oshimole ya kasance cikin masu nuna adawa da dokar.
To sai dai mataimakin shugaban majalisar dattawan, Sanata Barau Jibril ya yi watsi da bu?atar sanata Oshimolen, yana mai cewa ?orafin sanatan ya sa?a wa dokar majalisar saboda ?orafin ya zo ne bayan majalisar ta amince da ?udurin.
