Mun Shirya Gamuwa A Kotu Da Duk Mai ?alubalantar Nasarar Tinubu – APC

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kwamitin ya?in za?en Jam’iyyar APC mai mulki ya mayar wa ?an takarar Jam’iyyar Labour Peter Obi martani bayan da ya yi barazanar zuwa kotu domin ?alubalantar sakamakon za?en shugaban ?asar da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu nasara.

Jam’iyyar mai mulkin ?asar, a martaninta, ta ce a shirye take ta ha?u da Obi a kotun.

?an takarar na Labour a taron manema labaran da ya yi a yau Alhamis a Abuja, ya yi i?irarin shi ne ya lashe za?en amma aka yi mur?iya a cewarsa.

Ya kuma ce zai tabbatar da cewa shi ne ya yi nasara.

Idan za a iya tunawa a ranar Laraba ne hukumar za?en Najeriya ta ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya ci za?en.

Amma da yake mayar da martani, daraktan ya?a labaran kwamitin ya?in za?en APC, Bayo Onanuga ya ce jam’iyyar ta yi maraba da matakin Obi na zuwa kotu.

Idan har yana da ya?inin zai gabatar da hujjojin da suka tabbatar an yi magu?i a za?en.

?an takarar jam’iyya mai mulki, APC, wato Bola Ahmed Tinubu, shi ne ya yi nasara a za?en shugaban ?asar inda ya samu ?uri’a miliyan 8.79, wato kashi 37 cikin ?ari na ?uri’un da aka ka?a.

Sai Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP wanda ya zo na biyu, da ?uri’a 6,984,520, wato kashi 29.07 cikin ?ari.

Yayin da Peter Obi ya zo na uku da ?uri’a 6,101,533, wato kashi 25.4 cikin ?ari.

Shima a nashi ?angaren ?an takarar shugabancin ?asa na babbar Jam’iyyar adawa ta PDP Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewar bai gamsu da sakamakon zaben ba kuma zai garzaya kotu domin ?alubalantar nasarar Tinubu.

Sai dai yace ?alubalantar da ya ke yi wa sakamakon za?en ba na a mutu ko ayi rai bane, inda ya sha alwashin amincewa da hukuncin Kotu.

Related posts

Leave a Comment