Za Mu Kalubalanci Nasarar Tinubu A Kotu – Jam’iyyar Labour

Jam’iyyar Labour Party (LP) mai adawa a za?en shugaban ?asa na Najeriya ta bayyana cewa za ta ?alubalanci sakamakon za?en da ya bayyana Bola Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya yi nasara.

Yayin da yake jawabi a Abuja a yau Laraba, ?an takarar mataimakin shugaban ?asa a jam’iyyar LP, Datti Baba Ahmed, ya jaddada cewa akwai kura-kurai a za?en.

“Mun shiga za?en a matsayin LP kuma mun yi nasara da sunan LP,” a cewarsa. “Kuma za mu ?waci ha??inmu da sunan LP”.

Tun a ranar Talata jam’iyyun adawa na PDP da LP da ADC suka yi watsi da sakamakon a wani taron ha?in gwiwa, suna masu cewa hukumar za?e ta Inec ta gaza saka sakamakon a rumubun IReV da zai sa a gan shi ta shafin hukumar na intanet.

Peter Obi na LP ne ya zo na uku a za?en da ?uri’u 4,223,277, inda Atiku Abubakar na PDP kuma yake biye wa Tinubu da ?uri’u 6,301,741.

Related posts

Leave a Comment