Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Na Kara Karfi A Kaduna

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ayyukan ‘yan Bindiga na ?ara ?amari, bayanai sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun sake kai hari ?auyen Sabon Gero da ke ?aramar hukumar Chikum a jihar Kaduna, sun kashe jami’an tsaron sa kai guda biyu.

Yayin harin, yan ta’addan sun kuma sace mutane maza da mata da suka ha?a da mai ba da magunguna da matarsa suka rankaya dasu dokar daji.

Sai dai wasu bayanai sun nuna cewa mutum Shida daga cikin wa?anda maharan suka sace sun yi nasarar ku?utowa daga hannun yan bindigan.

A cewar wani shaidan gani da ido wanda ya nemi a ?oye sunansa yace lamarin ya faru ne da misalin ?arfe 1:00 na daren Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022.

“Wasu daga cikin mu ba su yi bacci ba suna harkokin dake kansu lokacin da muka fara jiyo karar harbe-harben bindiga. Yan bindigan sun kutsa gidajen mutane suka tasa su, suka ha?a da wasu masu kokarin guduwa.”

“Na gano cewa an kashe dakarun JTF mutum biyu a harin yayin da suka yi kokarin hana yan bindigan sace mutane.”

Yayin da aka tuntu?i kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya ce zai kira daga baya amma ba shi da masaniya a dai-dai lokacin da muke ha?a wannan rahoton.

Related posts

Leave a Comment