Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar batun wanda zai zama abokin takara wato mataimaki ga Alhaji Atiku Abubakar ?an takarar shugaban ?asa da PDP ta tsayar a zaben 2023, ya ?auki sabon salo.
Jam’iyyar PDP tare da ha?in guiwar ?an takaran sun shirya wasu matakai da zasu taimaka wajen zakulo abokin takara wanda masoyan PDP da ‘yan Najeriya zasu kar?e shi hannu biyu.
Majiyar ta kara da cewa kwamitin gudanarwa na PDP na ?asa karkashin shugaba, Dakta Iyorchia Ayu, da kwamitin amintattu karkashin Sanata Walid Jibrin suna kokarin cusa mutane daban-daban.
Shugaban Amintattu Sanata Walid Jibrin, a wata sanarwa ya ce kwamitinsa a shirye yake ya taimakawa wa ?an takara wajen zakulo amintaccen mataimaki daga yankin kudancin Najeriya.
“Kwamitin mu zai taimaka wa Jam’iyya da kuma wazirin Adamawa shi kansa domin za?ulo amintaccen mataimakin shugaban ?asa daga yankin kudancin Najeriya.”
Kwamitin Amintattu (BOT) ya yi hannun riga da kwamitin gudanarwa (NWC ) Amma majiyar ta ?ara da cewa taimakon da BOT ya shirya bada wa zai iya yin hannun riga da tsarin kwamitin gudanarwa NWC wan?anda ke kokarin jan ragamar ?auko wanda zai takara da Atiku a 2023.
Gwamna Wike na jahar Ribas shi ne ya zo na biyu a bayan Atiku Abubakar da kuri’u 237 kuma yana daga cikin mutanen da ake hasashen ba mukamin.
