Rahotannin daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewar Shugaban kungiyan mafarauta da yan vigilante na yankin arewa maso gabas Bala Yohanna ya ce ‘ya’yan tawagarsa sun kashe wani kwamandan Boko Haram da mataimakinsa da wasu mayaka a Borno.
Yohanna, wanda ya bayyana hakan a hira da aka yi da shi a ranar Talata da manema labarai, ya ce an yi artabu tsakanin yan ta’adda da mafarauta a kauyen Shaffa Taku da ke karamar hukumar Damboa a Borno a ranar Litinin.
Ya kara da cewa an kwato babura da kuma bindigogi kirar AK-47 daga hannun yan ta’addan.
“Mun samu bayanan sirri daga wurin wasu da suka fada mana yan ta’addan na damun garuruwansu makwanni biyu da suka gabata,” “Bayan samun bayanan, na tattara tawaga ta kuma muka dira wurin da yamma a Shaffa Taku, wani gari da mutane suka tsere daga cikinsu a Damboa.
“Mun yi sa’a, muka hangi yan ta’addan kimanin su 20, kan babura. Muka yi musayar wuta da su kuma muka kashe kwamandansu da mataimakinsa, yayin da saura suka tsere da rauni. “Mun kuma kwato babur daya da AK-47 guda daga hannun yan ta’addan.
Na sanar da jami’an tsaro na bataliya 231 a Biu, kuma za mu hadu a yau domin mika musu AK-47 din da babur ?in.”
Yohanna ya kuma ce a halin yanzu mafarautan sun kama wasu Mutane da ake zargin suna kai wa yan ta’addan kayan abinci. A cewarsa, an kama wadanda ake zargin da kudi Naira miliyan 6.05 a wani kauye a karamar hukumar Hawul. Ya ce an mika mutanen da aka kama ga jami’an tsaro domin daukan mataki na gaba.
