Za Mu Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotu – Kungiyar ASUU

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?ungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta sha alwashin ?aukaka ?ara game da hukuncin kotun ?a’ar ma’aikata, wanda ya umarci Malaman jami’a su koma bakin aiki.

An ruwaito ?ungiyar na cewa tuni ta fara tattara lauyoyi bisa jagorancin sanannen lauya mai fafutukar kare ha??in ?an adam, Femi Falana (SAN), domin shigar da ?ara a gaba.

Shugaban ASUU na shiyyar jihar Legas, Adelaja Odukoya, a wata sanarwa da ya fitar bayan Kotu ta yanke hukunci, ya roki mambobin ?ungiyar su kwantar da hankulansu kuma su ?aura ?amarar ya?i har karshe.

An jiyo shugaban ASUU na ?asa, Farfesa Emmanuel Osodeke, a cikin sanarwan yana mai rokon fusatattun lakcarori su kwantar da hankalinsu, babu wani abun damuwa kan umarnin su koma aiki.

“Ya kamata Mambobin mu su kasance a shirye su ha?a kai. Duk mutanen da kansu a ha?e yake babu mai yin nasara a kansu.” inji Osodoke.

Related posts

Leave a Comment