Hanani Takara: Za A Yi Tabare Kowa Ya Rasa – Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC na kasa Bola Ahmad Tinubu, ya ce ba wanda zai janyewa cikar burinsa na zama Shugaban kasa, ya kuma yi gargadin cewar matukar ba’a zabe shi a dan takara ba gara kowa ya rasa.

Shugaban kasa Muhammad Buhari, wanda a yanzu haka yake birnin Spain yace, “Jam’iyyar APC ba za tayi zaben fidda gwani ba, za a fitar da ?an takara ne ta hanyar masalaha kamar yadda aka yi a lokacin samar da sabon shugaban Jam’iyyar a matakin kasa.

A zaman yau da akayi wanda Buhari ya jagoranta da gwamnonin APC kafin ya tafi kasar Spain, an ruwaito cewar, An watse baranbaran tsakanin gwamnonin APC kan wanda zai yi takarar shugaban kasa a 2023, inda gwamnonin Arewa suka ce dan takarar shugaban kasa daga yankin Kudu ba zai iya kada Atiku Abubakar ba, a don haka dole sai dai a ba dan ?ankin Arewa takara.

Related posts

Leave a Comment