Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Tafka Ta’asa A Birnin Gwari

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Yan bindiga sun kashe mutane biyar ciki har da wani malamin makaranta a hanyar Layin Lasan Tabanni da ke karamar hukumar Birnin Gwari dake jihar.

An tattaro cewa yan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutane 16 a kauyukan Dogon Dawa, Layin Mahuta, da Tabanni da ke yankin gabashin karamar hukumar. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kungiyar kula da harkokin tsaro da shugabanci na yankin Ibrahim Abubakar Nagwari.

Kungiyar ta ce lamarin ya afku ne a lokuta mabanbanta tsakanin 14 da 19 ga watan Maris, na wannan shekara da muke ciki ta 2022.

Kungiyar ta bayyana cewa a ranar 14 ga watan Maris, yan bindiga sun kashe wani Haruna Tanko Dogon Dawa da wasu mutane biyu a hanyar Dogon Dawa zuwa Zariya. Nagwari ya ce: “An kuma yi garkuwa da wasu mutane takwas a wannan hanyar.

A Layin Mahuta (Tabanni), an kashe wani Abdullahi Abubakar wanda yake malamin makaranta ne a hanyar Layin Lasan Tabanni a ranar 16 ga watan Maris. “A ranar 17 ga watan Maris, an kashe wani tsoho dan shekara 70 sannan aka sace wasu mata bakwai a Layin Mahuta Tabanni.

An kuma yi garkuwa da wasu mutum biyu a tsohon Tabanni.” Shugaban kungiyar ya kara da cewar a yankin Randagi, yan bindiga sun saki mutane 32 daga cikin 46 da suka sace a makwanni uku da suka gabata a Unguwar Bula da Ijinga bayan an biya kudin fansa naira miliyan 16.

Ya bukaci jami’an tsaro da su dinga amsa kiran gaggawa a kewayen gudunmar Dogon Dawa, Kuyello, Tabanni, Kutemashi da Birnin Gwari, domin samun sau?in lamarin.

Sai dai kuma, shugabar karamar hukumar, Hajiya Ummah K. Ahmed, wacce ta tabbatar da kisan malamin da raunata wani, ta ce bata san da labarin sauran hare-haren da sace-sacen mutane da kungiyar ta ambata ba.

Related posts

Leave a Comment