Neja: Dan Majalisa Ya Sha Da Kyar A Hannun Matasa

Labarin dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewar Honorabul Musa Suleiman Nasko, dan majalisa mai wakiltan karamar hukumar Magama ta jihar Neja ya sha da kyar a hannun al’umman mazabarsa biyo bayan ruwan duwatsu da wasu fusatattun Matasa suka yi mishi.

A wani bidiyo da aka ya?a a kafafen sadarwa na zamani an gano yadda mutanen mazabarsa suka dunga jifarsa da duwatsu suna ihu shi kuma ya ranta cikin na kare.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne bayan dan majalisar ya ziyarci mazabar tasa domin jajantawa mutanen garin Magama wadanda rikicin ‘yan bindiga ke addabar su.

A garin Magama ne ‘yan bindiga suka kashe jami’an tsaro ciki har da shugaban yan sandan yankin wato DPO mai kula da garin Nasko.

Yana a hanyarsa ta fita daga garin ne bayan ya gana da iyalai, shugabannin addini da ‘yan sanda a Magama, lokacin da mutanen suka far masa da duwatsu.

A cikin bidiyon, an jiyo muryoyin wasu mutane suna fadin ‘Ba ma yi, Ba ma yi. Mu jefi Shege, dan shegiya kawai, Shege Dan Bura Uba! Ka ci Ubanka! Ba Ma yi. Ku jefe shi.’

An kuma jiyo karar harbi wanda ake zaton masu tsaron dan majalisar ne ke yinsa a iska domin tarwatsa mutanen da suka kai masa farmaki.

Related posts

Leave a Comment