Hana Kiwo A Kudu: Rayuwar Fulani Za Ta Shiga Ukuba – Miyyeti Allah


Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyatti Allah ta ce hankalin mutanen ta ya matukar tashi kan dokar da Majalisar dokokin jihar Enugu ta zartar na hana kiwo a fadin jihar.

Dokar ta zo bayan yarjejeniyar da gwamnoni kudancin kasar sha bakwai suka cimma, kan cewa daga 1 ga watan Satumbar dokar ta soma aiki.

Miyetti Allah ta ce akwai bukatar masu fada a ji su shigo cikin lamarin domin samun maslaha.

Related posts

Leave a Comment