Badala: Gwamna Tambuwal Ya Bada Umarnin Rushe Unguwa A Sokoto

Rahotanni daga birnin Sokoto Birnin Shehu na bayyana cewar Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da umarnin rusa wata unguwa da ke wajen babban birnin jihar nan take, biyo bayan zargin ayyukan ba?ala a Unguwar.

Aliyu Sidi Lamido wanda shi ne mai bai wa gwamnan shawara kan tsara birane, ya shaida wa manema labarai cewa matakin ya biyo bayan ?aurin sunan da unguwar da ake kira Raymond Village ta yi.

Ya ce unguwar ta zama matattarar “yan fashi da masu safarar miyagun ?wayoyi da safarar ?an Adam da Karuwai da sauran harkokin ba?ala.

Gwamnan ya ba da umarnin ne bayan wata ziyarar ba-zata da ya kai unguwar ranar Talata tare da rakiyar shugabannin hukumomin tsaro.

Related posts

Leave a Comment