Sojojin Mali Ragwaye Ne – Shugaban Nijar

Al’ummomin Jamhuriyar Nijar da na Mali na ci gaba da cacar baki kan shagu?en da shugaban Nijar ?in ya yi game da sojojin da ke mulkin ?asar ta Mali.

Shugaba Mohamed Bazoum ya soki sojojin da ke mulkin Mali yayin da yake halartar taron ?asashen ?ungiyar G5 Sahel a Faransa ranar Juma’a, 9 ga watan Yuli.

“Ya zama dole mu hana sojoji hawa mulki saboda suna da rauni a fagen daga wurin da ya kamata su kasance,” in ji Bazoum yayin da yake magana game da ?asar Mali.

Kalaman nasa sun jawo zazzafar mahawara a shafukan sada zumunta tsakanin al’umomin ?asashen biyu, a cewar wakiliyar BBC a birnin Yamai Tchima Ila Yusufu.

A martaninta, gwamnatin soja ta Mali ta gayyaci jakadan Nijar a Mali, Mamoudou Moumouni, domin bayyana masa damuwarta.

Sai dai yayin wata hira da kafar yada labarai ta gwamnati Shugaba Mohamed Bazoum ya nuna takaicinsa kan yadda ‘yan Mali suka ?auki wa?annan kalamai nasa.

Related posts

Leave a Comment