Najeriya Ta Cimma Nasara Duk Da Manyan Kalubalen Da Ta Fuskanta – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya ce ?asar Najeriya “ta yi sa’a” da har yanzu ba ta rabe ba duk da irin ?alubalen da aka fuskanta da ka iya wargaza ta a tsawon lokaci.

Buhari ya bayyana haka ne lokacin da yake kar?ar rahoton Kwamitin Taron Tsaro na ?asa da aka yi ranar 26 ga watan Mayun 2021 daga Majalisar Wakilai.

‘Yan majalisa ne suka gabatar wa da shugaban rahoton ?ar?ashin jagorancin Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila ranar Talata.

“Najeriya ?asa ce mai sa’a kuma ya kamata mu yi wa kanmu murna, duk da barazanar da muka fuskanta da ka iya raba kanmu,” in ji shugaban cikin wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar.

Buhari ya shawarci shugabanni da su girmama al’umma na ?asa da na sama ta yadda “[mutanen] za su lazumta wa kansu mayar da alherin da aka yi musu”.

Ya ci gaba da cewa girmamawa ga mutane ita ce “a ?yale su su za?i wanda suke so a matsayin shugbansu ba tare da nuna bambancin jam’iyya ko addini ba”.

Related posts

Leave a Comment