An bayyana cewar babu shakka gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal shine mafi cancanta da zama shugaban kasa a shekarar zabe ta 2023 idan aka kwatanta shi da sauran ‘yan takara.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani manazarcin harkokin siyasar Najeriya Alhaji MD Yusuf Naziya lokacin da yake tsokaci dangane da halin siyasar Najeriya a kakar zabe dake ta 2023.
MD Naziya ya cigaba da cewa irin nagarta da gogewar da gwamna Aminu Tambuwal ke da ita ta sanya yayi wa sauran ‘yan takarar shugabancin kasa fintikau ta fuskar cancanta.
?an siyasar ya cigaba da cewar gogewa da ?aga darajar Jihar Sokoto da Najeriya gaba ?aya da Aminu Tambuwal a mu?amin Gwamna da Kakakin Majalisar Tarayya ya zamana doke a sallama mishi.
“Tambuwal matsayinshi na matashi wayayye mai ilimi irin shi ne ?asa take bu?ata, bisa ga halin da ake ciki yanzu Najeriya ba ta bukatar ri?on tsoho, mutum mai jini a jika kamar Tambuwal ake da bukata.
“Na tabbatar Tambuwal ya cika dukkanin sharuddan da ake da bukata, mutumin da ya rike majalisar kasa sannan komai ya tafi daidai babu matsala, sannan yana matsayin gwamna ya taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da jiha gaba, irin wannan mutumi idan ya kai ga matsayin shugaban kasa nasarar da zai kawo mai yawa ce.
