Uwargidan shugaban Faransa, Brigitte Macron, za ta shigar da ?ara kan wani zargin da ake ya?awa a intanet cewa ta sauya jinsinta zuwa mace bayan an haife ta namiji.
An wallafa labarin ne a wani shafin masu tsauttsauran ra’ayi tun a watan Satumba wanda wasu suka ci gaba da ya?awa.
Daga cikin masu ya?awa har da masu adawa da mijinta shugaba Emmanuel Macron da suka ?unshi masu adawa da rigakafi.
Brigitte Macron tana da ?a?a uku manya da ta haifa a aurenta na farko.
A jita-jitar an yi i?irarin cewa an haife ta namiji ne aka ra?a mata sunan Jean-Michel Trogneux. Sunan ya kara?e shafukan sada zumunta inda aka ambaci sunan sama da 10,000 a Twitter.
