2023: Sabuwar Gwamnati Za Ta Gaji Bashin Triliyan 77 Daga Gwamnatin Buhari

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugabar Ofishin Kula da Basuka a Najeriya Patience Oniha ta ce duk gwamnatin da za ta gaji ta Shugaba Muhammadu Buhari a ?arshen watan Mayu za ta tarar da bashin da ya kai kusan naira tiriliyan 77.

Ta bayyana haka ne ranar Laraba yayin da take amsa tambayoyin manema labarai game da kasafin ku?in ?asar na 2023, wanda gwamnatin za ta cike gi?insa ta hanyar ciyo bashi.

Ministar Ku?i Zainab Ahmed ta ce za a samu kashi 22 cikin 100 na ku?in shigar da aka yi hasashe ta hanyar cinikin man fetur, yayin da za a samu kashi 77 daga wasu harkokin daban.

Don cike gi?in, ministar ta ce sai an kar?o bashin naira tiriliyan 7.04 a cikin ?asar da kuma tiriliyan 1.76 daga ?asashen waje. Haka nan za a kar?o tiriliyan 1.77 daga ?ungiyoyin ?asa da ?asa, da kuma sayar da kadarorin gwamnati da za su samar da naira biliyan 206.

A ranar Talata ne Shugaba Buhari ya saka hannu kan kasafin ku?in na 2023 kan sama da naira tiriliyan 20, wanda ke da gi?in tiriliyan 11.

Related posts

Leave a Comment