Yayin da saura makonni takwas a yi za?en shugaban ?asa da na ‘yan majalisar tarayya, kuma saura makonni goma a yi za?en gwamnoni, NNPP na ci gaba da samun tagomashi a Jihar Gombe.
Farkon wannan makon ne Babban Mai Binciken Ku?in PDP na Jihar Gombe, Honorabul Mahmoud Mohammed Wafa ya fice daga jam’iyyar, ya koma NNPP.
Wafa ya bayyana ficewar ta sa ce a lokacin da ya kai wa ?an takarar gwamnan Gombe na NNPP, Khamisu Mailantarki ziyara a gidan sa da ke Abuja.
Ya ce ya shiga NNPP ne domin a ha?a hannu dashi a ceto Jihar Gombe daga hannun gwamnatin APC, wadda ya ce ya ?as?antar da jihar Gombe a idon fa?in ?asar nan baki ?aya.
“Na shigo NNPP ne bisa la’akari da na yi cewa akwai bu?atar a ha?a hannu a ceto Jihar Gombe daga hannun APC. Sannan kuma ita PDP tun bayan za?en fidda gwani a shekarar da ta gabata ta samu gagarimar matsala. Saboda haka APC da PDP ?in duk ba za su iya samar mana shugabanci na gari a Gombe ba.”
“Amma idan mu ka waiwaya baya dangane da tasirin da Mailantarki ya yi a baya, to shi ne zai samar da nagartaccen shugabancin da zai bun?asa Gombe bayan za?en 2023.”
Tun da za?en 2023 ya gabato ne mambobi da wasu jiga-jigan APC da PDP ke da tururuwar ficewa su na komawa NNPP.
Ko a farkon wannan makon sai da wasu shugabannin PDP daga ?ananan hukimomin Funakaye da Dukku, su ka fice daga PDP su ka koma NNPP.
