Sanannen Dattijon nan mazaunin Jihar Kaduna kuma Shugaban kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya Farfesa Ango Abdullahi, ya yi tsokaci kan halin da Siyasar Najeriya ke ciki, da kuma irin zabin da ya kamata ‘yan kasar su yi.
A wata tattaunawa da ya yi da manema ta gidansa dake birnin Zazzau Ango Abdullahi ya bayyana ra’ayinsa cewa, sam ba ya goyon bayan tsarin siyasar karba-karba tsakanin shiyyoyi kamar yadda wasu jama’a ke ta hankoron haka a Najeriya.
Farfesa Ango Abdullahi yace abu mafi kyau shi ne ‘yan kasar su mai da hankali a zaben 2023 domin samar da shugaban da zai share hawayen ‘yan Najeriya. Ya bayyana a fili cewa, matukar ‘yan Najeriya basu mai da hankali ba, za su sake zaban shugabannin da zasu gasa musu aya a hannu kamar yadda ake gani a yanzu.
“Maimakon ’yan Najeriya su maida hankali wajen nemo mai hali nagari da zai zo ya magance mana matsalolinmu, sai magana suke kan wace kabila ce za ta samar da shugaban kasa.”
Da aka tambaye shi game da siyasar karba-karba tsakanin Kudu da Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya ce sam kundin tsarin kasar bai kawo hakan ba saboda haka babu dalilin batun.
Ya kuma ce, jam’iyyar PDP ce ta lalata tsarin da jam’iyyun siyasa ke dashi na karba-karba a kasar inda ya kara da cewa: “Lokacin da PDP ta yi tsarin karba-karba, ta ci amanar tsarin.
Amma babu laifi a Majalisar Dokoki ta kasa idan ’yan siyasa sun yarda a cikin su su horar da kansu cewa za su yi hakan a matsayinsu na mutanen kirki. ” ‘Yan siyasa sune suka kashe tsarin karba-karba a PDP. Hasali ma PDP da kanta ta kashe tsarin, ba su bi shi ba.”
Da aka tambaye shi game da mika kujerar mulki yankin Kudu kamar yadda wasu ‘yan PDP ke da ra’ayi, Ango Abdullahi ya ce: “Buhari ba ?an PDP bane. ?an APC ne kuma bai zo karkashin tsarin karba-karba da PDP ta ayyana ba kuma ya ce jam’iyyarsa ba ta da wani tanadi na tsarin karba-karba.”
