Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele ya ce bai yanke shawarar tsayawa takarar shugabancin Najeriya ba tukunna a babban za?en 2023.
Mista Emefiele mai shekara 60 na mayar da martani ne bayan rahotannin da suka kara?e kafofin ya?a labarai a ciki da wajen ?asa cewa ya sayi fom ?in takarar ranar Juma’a.
“Ina godiya da sha’awar da wasu ?ungiyoyi ke nunawa gare ni don na fito takarar shugaban ?asa,” in ji shi. “Sai dai idan na yanke hukuncin neman takarar zan yi amfani da ku?in da na tara daga aikina na banki tsawon shekara 35 don sayen fama-faman.”
Ya ?ara da cewa “wannan babban mataki ne da ke bu?atar taimakon Allah: nan da ‘yan kwanaki kuma Allah zai yi min jagora,” cikin wani sa?on Twitter a ranar Asabar.
Wasu daga cikin wa?anda suka ayyana yin takara a APC sun ha?a da Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo da kuma tsohon Gwamnan Legas Bola Tinubu.
