Harin Jirgin Abuja: Gwamnatin Kaduna Ta Bada Diyyar Miliyan 18

Rahoton dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Sakataren Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar KADSEMA, Muhammed Mukaddas ya bayyana yadda gwamnatin Jihar Kaduna ta amince da bayar da Naira Miliyan 18 ga mutane 9 wadanda mummunan harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya ritsa da su.

Mukaddas ya bayyana hakan ne a ranar Laraba inda ya ce a ranar 19 ga watan Afirilu gwamnatin ta amince da bayar da Naira Miliyan 2 ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu ta dalilin harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Mukaddas ya ce gwamnan ya amince da biyan mutane 22 da suka raunana dalilin harin, inda ya ce za a ba ko wannensu N250,000.

Sakataren KADSEMA ya ce ba an biya su kudaden don biyansu asarorin da suka tafka ba ne, an bayar ne don tallafa musu. Mukaddas ya ce amfanin hukumarsu kenan, kawo taimakon gaggawa idan bukatar hakan ta taso.

“An kira mutane 369 don a tallafa musu wurin kwantar musu da hankali, mutane 264 ne suka amince da tallafin kuma har an ba su.” Ya bayyana yadda aka sanar da hukumar wacce cikin gaggawa aka sanar da manyan ma’aikatan gwamnati da duk wadanda suka dace su sani, daga nan suka hada gwiwa wurin taimako tare da jami’an tsaro.

“Mun samar da motoci don kwashe mutane daga wurin, kafin mu isa sojoji sun fara kwashe mutane, daga nan ne muka fara kwashe gawawwaki da kuma wadanda suka raunana yayin da muka dauki mutum daya wanda ya gudu daga hannun masu garkuwa da mutane.”

“Mun ajiye gawawwakin a asibitin 44 NARH, yayin da muka kai wasu asibitin St. Gerald don a duba lafiyarsu. Sannan muka samar da hanyar tattaunawa da ‘yan uwan wadanda suka bata don samun bayanai akansu.”

Related posts

Leave a Comment