Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar za?e mai zaman kanta ta kasa ta ce jam’iyyun siyasa da ke son shiga babban zaben 2023 za su iya fara gudanar da zaben fitar da gwani a hukumance.
Hukumar ta ce daga ranar 4 ga wannan watan zuwa 3 ga watan Yunin 2022 aka ke?e domin jam’iyyun siyasa su gabatar da za?ukan cikin gida tare da warware dukkan wani rikici da ka iya tasowa sakamakon za?ukan.
Jami’a a hukumar za?en Hajiya Zainab Aminu Abubakar ta ce lokacin da aka ware na fitar da ?an takara na cikin kundin dokokin za?e na ?asar.
Ana son jam’iyyun siyasar su tsayar da ?an takara tare da warware duk wani sa?ani kafin cikar wa’adin da aka ?ayyade.
