Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar ?ungiyar Jamaatul Nasrul Islam ta yi tir da harin dayan bindiga suka kai kan jirgin kasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a makon jiya.
Cikin kalamai na rashin jin dadin abin da ya faru, Kungiyar ta ce babban ha??in da ke wuyan gwamnati shi ne kare rayukan al`umma, kuma alama ce ta rauni a ce gwamnati ta gaza yin hakan.
Dr Khalid Abubakar Aliyu babban sakataren kungiyar ya ce an da?e ana ruwa ?asa na shanye wa, domin an da?e ana fama da matsalar tsaro amma ba sau?i.
Ya ce: “Wurare da yawa an hana noma da cin kasuwanni, wanda ke nuna kamar gwamnati ta gaza, lamarin da kan iya jefa al’umma cikin wani hali.”
