2023: Ina Da Tabbacin Osinbajo Ne Shugaban Kasa – Sanata Gaya

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sanata mai wakiltar Kano ta kudu, Sanata Kabiru Gaya, ya kar?i ragamar kungiyar cigaba (TPP), gamayyar kungiyoyin magoya baya masu ya?a manufar mataimakin shugaban ?asa, Yemi Osinbajo.

Da yake jawabi a wurin taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Sanata Gaya, ya ce burin Osinbajo ba na ?ashin kansa bane, amsa kiran al’umma ne na tsayawa takara.

Sanatan ya ?ara da cewa ya na da kwarin guiwa Osinbajo ne zai gaji kujerar shugaba Buhari a za?en 2023, domin ?orawa daga inda Buhari ya tsaya na ciyar da ?asa gaba.

“Ba tare da wata tantama ba, ina da ya?inin cewa duk wasu masu hankali anan sun fahimci tare da tabbatar da nagarta da cancantar Farfesa Yemi Osinbajo.” “Ta hanyar za?en mutum kamar Osinbajo, wanda ya san kalubalen da muke fuskanta fiye da tunani da kuma sanin dabaru da hanyoyin magance su, muna da babbar damar cigaba cikin ?ankanin lokaci.”

“Ina da kwarin guiwar cewa da karfin ikon Allah mai girma da ?aukaka da kuma ruwan kuri’un miliyoyin ‘yan Najeriya a fa?in sassan ?asar nan shida, Osinbajo ne zai gaji shugaba Buhari ranar 20 ga watan Mayu, 2023.”

Related posts

Leave a Comment