Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce kasashen Turawa sun fi nuna damuwa da halin da Jihar Borno ke ciki na ta?ar?arewar tsaro da barazanar ?ungiyar ta’addanci ta Boko Haram fiye da ?asashen Larabawa.
Zulum ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin jakadan Falasdinawa a fadar gwamnatin jihar Borno dake birnin Maiduguri cikin makon nan. A cewar gwamnan, babu wata kasar Larabawa a baya da ta ba Jihar Borno tallafin da kasashen Turai suka bayar Sakamakon ?alubalen hare-hare na Boko Haram da sauran ayyukan ta’addanci masu kama da haka.
Sai dai Gwamnan ya jinjinawa yankin na Falas?inu da zama ?aya tamkar da dubu a yankin gabas ta tsakiya wajen nuna damuwa da kulawa da halin da jama’ar Jihar Borno da makwabtan ta ke ciki na matsalar tsaro.
“Ni mutum ne mai son yin abu a aikace. Ina amfani da zahirin abinda na gani a ?asa. “Cikin shekarun da muke fama da ?alubale, mun kar?i tallafi daga Birtaniya da wasu ?asashen Turai da Amurka, Canada har daga Japan da suka nuna damuwarsu wajen tallafawa da magunguna da kayan abinci”.
“Larabawa ba su ta?a nuna damuwarsu gare mu ba. Ziyarar ka ta Ba mu kwarin gwiwa kan ku, muna matu?ar godiya” in ji Zulum.
Da yake maida jawabi Jakadan kasar na Falas?inu ya bayyana cewa “Akwai kamfanonin Falas?inawa da yawa a Najeriya da suke son aiki da gwamnatin Borno, a shirye muke da ha?in gwiwa da ku, a shirye muke da mu tallafe ku da duk abinda kuke son wanda za mu iya.”
Ambasadan ya kara da cewa, akwai da yawa yan Najeriya ciki har da yan asalin Borno da ke zaune a Falas?in har ma suke shiga gwamnati ake damawa da su.
