Labarin dake shigo mana daga Jihar Zamfara na bayyana cewa Hukumar yan sanda reshen jihar ta ce wasu mutum Bakwai ?an gida ?aya sun rasa rayukansu bayan sun ci abincin gargajiya ‘Dambu’ lokacin cin abincin dare.
Mai magana yawun hukumar yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, shi ne ya bayyana haka ga hukumar dillancin labarai ta ?asa (NAN).
Shehu ya ce tuni hukumar ta fara gudanar da bincike domin gano musabbabin rasuwar iyalan ?an gida ?aya a ?auyen Dambaza da ke ?aramar hukumar Maradun.
“Lamarin ya auku ranar Litinin jim ka?an bayan iyalan sun kammala cin abincin da aka shirya musu na dare.” “Hukumar yan sanda ta ?ibo irin abincin da suka ci domin gudanar da bincike kuma ina tabbatar wa al’umma cewa za mu fallasa sakamakon abinda muka gano ga manema labarai.”
Wani mazaunin ?auyen, Muhammad Kabir, wanda ke da kusanci da iyalan, ya shaida wa NAN cewa hudu daga cikin iyalan da suka ha?a da matan aure biyu da yara sun rasu nan take, yayin da ragowar mutum uku suka ce ga garin ku nan bayan kai su Asibiti mafi kusa.
