Da Dumi-Dumi: Atiku Ya Zabi Okowa Mataimaki

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Atiku Abubakar ?an takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar PDP, ya zabi Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Delta a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 mai gabatowa.

Kwamitin gudanar da ayyuka na jam’iyyar PDP a ranar Laraba ya zabi Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, a matsayin wanda zai kasance mataimakin ?an takarar shugabancin kasar Atiku.

Wasu manya a PDP an gano ba su aminta da Wike ba saboda tsananin kusancin mataimakin shugaban kasa da kujerar shugabancin Kasar.

Atiku ya sanar da zabin Okowa ne a ranar Alhamis a hedkwatar jam’iyyar PDP ta ?asa dake Abuja. Ya ce ya yanke wannan shawarar ne bayan dogon nazari da tattaunawa da masu ruwa da tsakin jam’iyyar.

“Ina farin cikin sanar da sunan Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin ‘dan takarar shugaban kasa. Ina hango tafiyar da kasar mu, tare da dukkan ‘yan Najeriya da kuma gina zaman lafiya, hadin kai da cigaba ga kowa,” ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Related posts

Leave a Comment