Matsalar Tsaro: Sama Da Katsinawa 13,000 Sun Tsallaka Nijar

Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwamna Aminu Masari ya bayyana cewa al’ummar Jihar Katsina sun ga bala’in ‘yan bindiga, a cikin mummunan tashin hankalin da aka shiga matsananciyar wahala.

Masari ya ce bala’i ya yi tsananin da an fatattaki mutane daga yankunan su, har ta kai sama da Katsinawa 13,000 sun yi gudun hijira zuwa cikin Jamhuriyar Nijar.

Katsina na daga cikin jihohin Arewa maso yamma da ‘yan bindiga su ka hana zaman lafiya.

‘Yan bindiga sun kashe dubban mutane a Katsina, Zamfara, Sokoto, Neja, Kebbi da Kaduna.

Sun kuma kar?i biliyoyin ku?a?en fansar wa?anda su ke yin garkuwa da su. Kuma sun kori dubban jama’a daga garuruwan su, sun kwashe masu dabbobi da kayan abinci, sun kuma hana su zuwa gona noma.

Related posts

Leave a Comment