Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon gwamnan Jihar Kano kuma ?an takarar shugaban ?asa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya ce Atiku Abubakar ya mance da zancen zai iya samun kuri’u miliyan 11m a 2023.
Kwankwaso ya ce ya kamata ace tsohon mataimakin shugaban ?asan ya ankara da cewa siyasar Najeriya ta canza salo a shekaru uku da suka gabata, ta wuce da tunanin shi.
Jagoran jam’iyyar NNPP mai kayan marmari ta ?asa ya yi wannan furucin ne ranar Talata a Abuja, jim ka?an bayan kammala tantance shi a matsayin ?an takarar shugaban ?asa a za?en dake tafe na 2023.
Ya ce a halin yanzun ‘yan Najeriya sun shiga taitayin su, sun waye fatan da suke su samu shugaba da zai kawo sauyi a ?asar nan kuma ya tafiyar da ita kan hanya mai kyau ba hauragiya ba.
Dangane da ikirarin ?an takarar da PDP ta tsayar, Atiku Abubakar, cewa yana da tabbacin kuri’u miliyan 11m a zaben 2023. An jiyo Kwankwaso na cewa: “A ina daga wurin su wa zai samu kuri’u miliyan 11m? wa ya kawo masa kuri’un? Mu ne nan muka jawo masa su.”
“Akwai rabuwar kai da yawa a ?asar nan kuma idan ba’a ?auki mataki da wuri ba Najeriya ba zata cigaba ba. Mun ga abinda ya faru a Kano yadda aka karkatar da kuri’u a 2019, haka ba zata faru a 2023 ba.”
“Yan Najeriya na bukatar wanda zai ceto ?asar su, don haka a 2023 Najeriya zata bukaci wanda ya cancanta, ‘yan Najeriya zasu bi bayan mutanen da zasu iya kuma mu zamu yi aiki da kowa ba tare da duba addini ko kabila ba.”
