Tsohon na hannun daman Shugaba Buhari kuma tsohon Mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar APC Injiniya Buba Galadima, ya yi Alla-wadai da yadda ake sama da fadi da kudin kasa karkashin Shugaba Muhammadu Buhari.
Galadima ya ce kama Akanta Janar, Ahmed Idris, wanda ake zargi da satar N80bn alama ce babba dake nuna gazawar gwamnatin Buhari mai ikirarin yaki da cin hanci da rashawa.
Dattijon ya bayyana hakan ne a hirarsa da tashar ChannelsTV. Yace: “Shin wai kun yarda mutumin nan na yaki da rashawa ya sa aka kama Akanta-Janar? Sau nawa ana kai masa karar Akanta Janar?” “Saboda abin ya wuce gona da iri ne yasa aka kamashi.
Wannan ba shi bane karon farko. Wa’adin Akanta-Janar ya kare amma ya barshi ya cigaba da zama a ofis.” “Shin wa’adinsa bai kare bane? Shekaru biyu da suka gabata? Me yasa ya barshi a ofis? Shin yana ji?a wasu makusantan Buhari da kudi ne?
Galadima ya ?ara da cewar Buhari ya kashe ?asa fiye da yadda ake zato kuma duk wanda ya gaji Buhari na da babban aiki a gabansa.
