2023: Arewa Ba Ta Da Zabin Da Ya Wuce Tinubu – Ganduje

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Ganduje, yace mutanen yankin arewacin Najeriya ba su da ?an takarar da zasu goyi baya wanda ya zarce Bola Tinubu a zaben 2023 dake tafe.

An ruwaito cewa Ganduje ya yi wannan furucin ne a wurin bikin kaddamar da kungiya magoya bayan Tinubu ‘Northern Youth Professionals for Tinubu’ wanda ya gudana a hanyar Ha?eja, Kano, ranar Litinin.

Gwamnan, wanda daraktan hukumar kula da ababen hawa ta jihar Kano, Dakta Baffa Babba Dan’agundi, ya wakilta, yace ya zama wajibi yan arewa su maida bikin da mutane kudu maso yamma suka yi musu a 2015.

A cewarsa, mutanen arewacin Najeriya, babu wani ?an takara da zasu za?a a za?en 2023 dake tafe sai Bola Tinubu. Ya ce: “Arewacin Najeriya ba su da wani za?i sai goyon bayan ?an takarar Yarbawa kuma Tinubu.

Idan na tambaye ku, ku fa?a mun mutumin da ya goyi bayan Buhari 100 bisa 100 na san Tinubu ne amsar.” “Lokaci ya yi zamu tabbatar da cewa mu ‘ya’yan halas ne iyayen mu suka haife mu mu yi mishi sakayya.

Lokaci ya yi kuma muna tare da takarar Bola Tinubu.” READ ALSO Abokai sun lakadawa mutumi dukan tsiya har ya mutu kan batan waya, aka ga wayar kasan Kujera

“Mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, na ?aya daga cikin masu goyon bayan wannan tafiya, don haka muna bayan Tinubu a 2023.”

Related posts

Leave a Comment