Gwamnatin Jihar Abiya ta fara biyan diyya ga mutanen da hari da aka kai a sabuwar kasuwar shanu ta Abia ya shafa a yankin kudu maso gabashin kasar.
Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Dr Okezie Victor Ikpeazu na jihar a ranar 20 ga watan Fabrairu ya gana da al’ummar Hausa-Fulani mazauna jihar kan harin.
Sarkin Hausawan Aba Shehu Bello ya shaida cewa “gwamnan ya fara da yin tir da harin da aka kai kafin ya tabo batun biyan diyyar.”
“Abin da gwamnatin ta biya bayan taron na ranar Lahadi shi ne diyyar dabbobin da aka kashe, ina ganin kimanin shanu 56 da awaki 50 ne.
“A kan kowacce saniya, gwamnati za ta biya N150,000 kuma za ta biya N50,000 kan kowace akuya, kuma gwamnan ya yi alkawarin bayar da naira miliyan biyu na diyya ga kowane ran mutum daya da aka kashe kuma ranar Alhamis za mu karbo kudin,” inji shi.
Shugaban al’ummar Hausawan ya kuma ta?o batun binne mutum takwas, wanda aka yi ranar Juma’a, inda ya ce mutum daya ne ya rage a dakin ajiyar gawa a wannan lokacin.
