Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin tarayya ta cire dokar hana fita ta tsakar dare da kuma taruwar jama’a a tarukan bikin aure da na wa?e-wa?e wa?anda aka saka da zimmar ya?i da annobar korona.
Kwamatin ya?i da cutar na shugaban ?asa ya ce an ?auki matakin ne sakamakon raguwar mutanen da ke kamwua da cutar a ?asar.
Najeriya ta saka dokokin ne tun bayan ?ullar annobar cikin ?asar a watan Fabarairun 2020.
Wata sanarwa daga kwamatin ta ce an kuma samu raguwar ha?arin ya?a sabon nau’in cutar.
Sai dai kuma, ya jaddada cewa wajibi ne mutane su ci gaba da saka takunkumi idan suna cikin wani rufaffen wuri amma bai zama lallai su saka ba idan suna bu?a??en wuri ko kuma fili.
An janye ?ayyadewar adadin mutanen da za su halarci wani taron addini amma kwamatin ya ce lallai ne a saka takunkumi a wurin.
