Malaman Addini Sun Taka Muguwar Rawa Wajen Jefa Najeriya Halin Da Take Ciki – Mahadi Shehu

An bayyana cewar malaman addini sun taka wata irin muguwar rawa wajen jefa Najeriya halin da ta tsinci kanta ciki na ta?ar?arewar tsaro da koma baya.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin sanannen ?an kasuwar nan mazaunin garin Kaduna Dr Mahadi Shehu a yayin wata tattaunawa da manema labarai da yayi a Kaduna.

Dr Mahadi ya kara da cewar wadannan Malaman Addini sune suka hau munbari suka yi ma wata Jam’iyya kamfe suka tsarkake ‘yan takarar ta, sannan a hannu guda suka kafirta wata Jam’iyya da ‘yan takararta.

“Matsalolin kasar nan kashi 7 cikin 10 wadannan malamai sune sila suna cigaba da holewa a yayin da sauran jama’a talakawa ke cikin kunci to al’amarin yazo ?arshe za?en 2023 ya kawo jiki, za muga malamin da ya isa ya hau munbari ya kafirta wani kan siyasa”

Dr Mahadi Shehu ya shawarci dukkanin ‘yan Najeriya Musulmi da Kirista da su kauce wa yin amfani da siyasa ta Addini da ?abilanci, su dubi wanda yake da inganci da zai iya kai ?asa ga nasara kawai, amma muddin ‘yan Najeriya za su cigaba da yin siyasa da nuna banbance banbance, babu sakamakon da za su samu sai damuwa da takaici.

Related posts

Leave a Comment