Karin Farashin Mai Zai Jefa ‘Yan Najeriya Cikin Talauci

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon Shugaban kasa na mulkin Soja, Janar AbdulSalami Abubakar, ya yi gargadi game da shirin kara farashin litan man fetur da gwamnatin tarayya ke shirin yi.

A jawabin da ya gabatar ranar Alhamis a taron tattaunawa kan halin da kasa ke ciki da Daily Trust ta shirya a Abuja, tsohon Shugaban yace hakan na da hadari. A cewarsa, sama da yan Najeriya milyan 18 yanzu haka na fama da bakin talauci da bai kamata ba kuma annobar COVID-19 ta sake tsananta lamarin.

“Matsalar tsaro ta lalata tattalin arzikinmu. Rashin aikin yi da kuma rashin samun isasshen kudi ga masu aiki ya yi muni. Sama da yan Najeriya milyan 18 na cikin talauci mara amfani.”

“Farashin kayan abinci na cigaba da hauhawa kuma yan Najeriya sun fara gaza siya. Duk da haka, ana shirin kara farashin man fetur kamar yadda aka sanar a Nuwamba. Dukkanmu mun san idan haka ya faru, za’a jefa miliyoyin yan Najeriya cikin talauci.”

Related posts

Leave a Comment