Rahotannin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Antoni Janar na ?asar nan kuma ministan shari’a, Abubakar Malami SAN, yace shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, ya ceci Najeriya daga rushewa cikin shekarar farko da kafa gwamnatinsa.
Abubakar Malami yace Buhari ya samu kasar nan a dai-dai lokacin da tattalin arziki ke gab da rushewa, wanda ka iya jawo watsewar ?asar baki ?aya kowa ya kama gabansa.
Ministan, wanda ya fa?i haka a wani shirin gidan Radiyo a jihar Kano, yace kowane bangare na tatattalin arzikin Najeriya ya samu koma baya kafin zuwa shugaba Buhari. Haka nan kuma Buhari ya ceci gwamnatocin jihohi daga matsi ta hanyar raba musu makudan kuda?e a lokuta daban-daban.
“Shugaban ?asa ya yi wannan duk a cikin abin da bai kai shekara ?aya ba; Ya ceci tattalin arziki daga mummunan fa?uwa, ba kasafai ake samun haka ba don ba kowane shugaba ne zai iya haka ba.” Ya ?ara da cewa shugaban bai tsaya iya nan ba, ya kirkiro abubuwa da dama da suka taimakawa yan Najeriya kamar tsarin N-Power da kuma tallafin COVID19.
A cewar ministan irin wa?an nan abubuwan da shugaba Buhari ya samar sun taimaka sosai wajen samar da aikin yi ga yan Najeriya da dama.
Game da lamarin tsaro kuwa, Malami yace Buhari ya ?auki tsaro da muhimmanci, inda ya ?auki matakan hana yan ta’addan Boko Haram cigaba da kai muggan hare-hare. “Kafin zuwan Buhari, akwai kalubale mai yawa a bangaren tsaro, amma yanzun mun samu nasarar hana kai hare-hare kamar na baya. An jima sosai kafin ka ji an kai hari kasuwa, ko wuraren ibada da sauran su.”
Kazalika ministan yace jajircewan da hukumomin tsaro suka yi a arewa maso yamma, yasa yan bindiga suka fara neman yadda za’ai sulhu da gwamnati.
