Zuwa Dubai Ya Fi Sauki Gareni Akan Zuwa Kasuwar Rimi – Rashida Mai Sa’a


Tsohuwar jarumar Finafinan Hausa Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a ta Kara nanata maganar ta, da ta yi a kwanakin baya in da ta bayyana cewar, zuwa kasar Dubai ya fi mata sauki, a kan zuwa kasuwar Rimi da ke bakin asibitin Murtala a cikin garin Kano.

Tun dai lokacin da ta yi wannan furucin a lokacin da gidan rediyon BBC suka yi hira da ita ne, jama’a suka yi ta yin magana a kan wannan kalamai na Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a, inda wasu suka rinka karyata ta, wasu kuma suna ganin ko dai ba ta san kasar Dubai din ba ne?

Sai dai a tattaunawar da aka yi da ita Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a, ta kara nanata maganar ta, ta in da ta ke cewa “Har yanzu Ina kan baka na, na zuwa Kasar Dubai ya fi mini sauki a kan zuwa kasuwar Rimi ta bakin asibitin Murtala, domin a sati zan iya shiga kasar Dubai sau biyu, amma ni har na manta rabon da na je kasuwar Rimi, domin idan a Mota zan je babu wajen da zan ajiye Mota ta, kuma ba zan iya zuwa a kasa ba, saboda cunkoson mutane, kuma a matsayina ta wacce duniya ta sani, ka ga zuwan ba zai zama mai sauki a wajena ba, ” inji ta.

“Amma idan zan tafi Dubai zan je ne na hau jirgi na yi tafiya ta ba tare da kowa ya san na yi tafiya ba, don haka ina nan a kan baka na, na zuwa kasar Dubai ya fi mini sauki a kan zuwa kasuwar Rimi da ke bakin asibitin Murtala

Related posts

Leave a Comment